1 Taku ta ƙare, ku da kuke zamansakewa a Sihiyona,Da ku da kuke tsammani kunazaman lafiya a Samariya,Ku da kuke manyan mutaneNa wannan babbar al'umma taIsra'ila,Waɗanda jama'a suke zuwa a gare suneman taimako!
2 Ku je ku duba a birnin Kalne.Sa'an nan ku zarce zuwa babbanbirnin Hamat,Har zuwa birnin Gat ta Filistiyawa.Sun fi mulkin Yahuza da Isra'ila ne?Ko kuwa, yankin ƙasarsu ya finaku?
3 Kuna ƙoƙari ku kauce wa wannanrana ta masifa,Amma ga shi, goyon bayan hargitsikuke ta yi,Ta wurin ayyukanku.
4 Taku ta ƙare, ku da kuke kwancekan gadajen hauren giwa,Kuna jin daɗin miƙe jiki a dogayenkujerunku,Ku ci naman maraƙi da na rago.