3 Kuna ƙoƙari ku kauce wa wannanrana ta masifa,Amma ga shi, goyon bayan hargitsikuke ta yi,Ta wurin ayyukanku.
4 Taku ta ƙare, ku da kuke kwancekan gadajen hauren giwa,Kuna jin daɗin miƙe jiki a dogayenkujerunku,Ku ci naman maraƙi da na rago.
5 Kukan so ku tsara waƙoƙi kamaryadda Dawuda ya yi,Ku raira su da garayu.
6 Da manyan kwanoni kuke shanruwan inabi,Ku shafe jiki da mai mafi kyau,Amma ba ku yin makoki sabodalalacewar Isra'ila.
7 Don haka, ku ne na fari da za a sa suyi ƙauraBukukuwanku da shagulgulanku zasu ƙare.
8 Ubangiji kansa ne ya rantse.Ubangiji Allah Mai Runduna ya ce,“Ba na son girmankai na jama'arIsra'ila.Ba na son fādodinsu.Zan ba da birnin da dukan abin dayake cikinsa ga abokan gābansu.”
9 Ko da a ce mutum goma ne suka ragu a gida guda, duk za su mutu.