1 Zofar ya amsa.
2 “Ayuba, ka ɓata mini rai,Ba zan yi haƙuri ba, sai na ba ka amsa.
3 Abin da ka faɗa raini ne,Amma na san yadda zan ba ka amsa.
4 “Hakika ka sani tun daga zamanin dā,Sa'ad da aka fara sa mutum a duniya,
5 Ba wani mugun mutum wanda ya taɓa daɗewa da farin ciki.