1 “Amma yanzu waɗanda na girme su, sai ba'a suke mini,Waɗanda iyayensu maza ba su fi karnukan da suke kiwon garken tumakina ba.
2 Wace riba zan samu ta wurin ƙarfin hannuwansu waɗanda ba su da sauran kuzari?
3 Saboda rashi da matsananciyar yunwa sun rame,Sai gaigayar ƙasa suke yi da dare, a cikin kufai.
4 Sukan tsinki ganyaye masu ɗaci na jeji su ci,Sukan ci doyar jeji.