2 Wace riba zan samu ta wurin ƙarfin hannuwansu waɗanda ba su da sauran kuzari?
3 Saboda rashi da matsananciyar yunwa sun rame,Sai gaigayar ƙasa suke yi da dare, a cikin kufai.
4 Sukan tsinki ganyaye masu ɗaci na jeji su ci,Sukan ci doyar jeji.
5 Aka kore su daga cikin mutane,Suka yi ta binsu da ihu kamar yadda ake yi wa ɓarawo,
6 Sai a kwazazzabai suke zamaDa a ramummuka da kogwannin duwatsu.
7 Suka yi ta kuka a jeji,Suka taru wuri ɗaya a cikin sarƙaƙƙiya.
8 Mutane ne marasa hankali marasa suna!Aka kore su daga ƙasar.