12 Amma idan ba su kasa kunne ba,Za a hallaka su da takobi,Su mutu jahilai.
13 “Waɗanda ba su da tsoron Allah a zuciyarsu,Suna tanada wa kansu fushi,Ba su neman taimako sa'ad da ya ɗaure su.
14 Sukan yi mutuwar ƙuruciya,Sukan ƙare kwanakinsu da kunya.
15 Zai kuɓutar da waɗanda suke shan tsanani,Ta wurin tsananin da suke sha,Yakan buɗe kunnuwansu ta wurin shan wahala.
16 Allah ya tsamo ka daga cikin wahala,Ya kawo ka yalwataccen wuri inda ba matsi,Abincin da aka yi na addaras aka jera maka a kan tebur.
17 “Ka damu ƙwarai don ka ga an hukunta mugaye,Amma hukunci da adalci sun kama ka.
18 Ka lura kada ka bar hasalarka ta sa ka raina Allah,Kada kuma ka bar wahalar da kake sha ta sa ka ɓata da mai fansarka.