13 Ya kuma haifi 'ya'ya maza bakwai, mata uku.
14 Ya raɗa wa ta farin suna Yemima, da ta biyun Keziya,da ta ukun Keren-Haffuk.
15 Duk ƙasar ba 'yan mata kyawawa kamar 'ya'yan Ayuba. Mahaifinsu kuwa ya ba su gādo tare da 'yan'uwansu maza.
16 Ayuba ya rayu shekara ɗari da arba'in bayan wannan, ya ga 'ya'yansa, ya ga jikokin jikokinsa har tsara ta huɗu.
17 Sa'an nan Ayuba ya rasu da kyakkyawan tsufa.