26 Raina na wucewa kamar jirgin ruwa mafi sauri,Da sauri ƙwarai kamar juhurma ya kai wa zomo sura.
27 Idan an yi murmushi,Ina ƙoƙari in manta da azabata,
28 Sai dukan wahalar da nake sha ta yi ta firgita ni,Na sani Allah ya ɗauke ni mai laifi.
29 Tun da yake Allah ya ɗauka, ni mai laifi ne,To, me zai sa in damu?
30 Ba sabulun da zai iya wanke zunubaina.
31 Allah ya jefa ni a kwatami,Har tufafina ma suna jin kunyata.
32 Da a ce Allah mutum ne,Da sai in mayar masa da magana,Da sai mun je ɗakin shari'a a yanka mana shari'a.