32 Waɗanda suka ta da alkawarin kuma, sarki zai ƙara dulmuyar da su ta wurin daɗin bakinsa. Amma waɗanda suka san Allahnsu za su tsaya da ƙarfi su yi wani abu.
33 Waɗansu daga cikin mutane waɗanda suke da hikima, za su wayar da kan mutane da yawa. Amma duk da haka za a kashe su da takobi, waɗansu da wuta, a washe waɗansu a kai su bauta.
34 Sa'ad da suka fāɗi ba za su sami wani taimakon kirki ba, mutane da yawa za su haɗa kai da su, amma da munafunci.
35 Waɗanda suke da hikima, za a kāshe su, don a tsabtace su, a tsarkake su, su yi tsab tsab, har matuƙar da aka ƙayyade ta yi.
36 “Sa'an nan sarki zai yi yadda ya ga dama. Zai ɗaukaka kansa, ya aza ya fi kowane allah. Zai kuma yi maganganu na saɓo a kan Allahn alloli, zai yi nasara, sai lokacin da aka huce haushi, gama abin da aka ƙaddara zai cika.
37 Ba zai kula da gumakan kakanninsa ba, ko begen da mata suke yi. Ba kuwa zai kula da kowane irin gunki ba, domin zai aza kansa ya fi su duka.
38 A maimakon haka zai girmama gunkin kagarai, gunkin da kakanninsa ba su ko sani ba, shi ne zai miƙa masa zinariya, da azurfa, da duwatsu masu daraja, da abubuwa masu tamani.