7 Ba za a daɗe ba, wani daga cikin danginta zai tasar wa sojojin sarkin arewa da yaƙi, ya shiga kagararsu, ya ci su da yaƙi.
8 Zai kwashe gumakansu ganima, da siffofinsu na zubi, ya kai Masar, tare da tasoshinsu na azurfa da na zinariya masu daraja. Zai yi shekaru bai kai wa sarkin arewa yaƙi ba.
9 Bayan wannan sarkin arewa zai kai wa sarkin kudu yaƙi, amma tilas zai janye, ya koma ƙasarsa.
10 “'Ya'yansa maza za su tara babbar rundunar yaƙi. Ɗayansu zai mamaye kamar rigyawa, har ya kai kagara wurin da abokan gāba suke.
11 Sarkin kudu zai husata ya kai wa sarkin arewa yaƙi, za a ba da rundunar sojojin sarkin arewa a hannunsa.
12 Ganin ya kashe sojoji masu ɗumbun yawa, sai ya yi girmankai, amma nasararsa ba mai ɗorewa ba ce.
13 Sarkin arewa kuwa zai tara babbar rundunar soja fiye da ta dā. Bayan waɗansu shekaru kuwa zai kama hanya da babbar rundunar soja, da kayan faɗa masu yawan gaske.