2 Waɗanda suka rasu za su tashi, waɗansu zuwa rai madawwami, waɗansu kuwa zuwa kunya da madawwamin ƙasƙanci.
3 Waɗanda suke da hikima za su haskaka kamar sararin sama, waɗanda kuma suka juyar da mutane da yawa zuwa adalci, za su zama kamar taurari har abada abadin.
4 “Amma kai, Daniyel, sai ka rufe maganar, ka kuma kulle littafin, har zuwa ƙarshen lokaci. Mutane da yawa za su yi ta kai da kawowa, ilimi kuma zai ƙaru.”
5 Sa'an nan ni Daniyel na duba, sai ga waɗansu biyu a tsaye, ɗaya a wannan gāɓa ɗayan kuma a waccan gāɓar kogin.
6 Dayansu ya ce wa mutumin da yake sāye da rigar lilin, wanda yake tsaye a gaɓar kogin, “Sai yaushe waɗannan abubuwan banmamaki za su ƙare?”
7 Sai mutumin da yake sāye da rigar lilin ɗin, wanda yake tsaye a gaɓar kogin ya ɗaga hannuwansa sama, sa'an nan ya rantse da wanda yake rayayye har abada, ya ce, “Za a yi shekara uku da rabi. Za a kammala waɗannan abubuwa, sa'ad da aka gama ragargaje ikon tsarkakan mutane.”
8 Na ji, amma ban gane ba. Sai na ce, “Ya shugabana, mene ne ƙarshen waɗannan abubuwa?”