26 Ma'anar wannan ita ce, MENE, wato Allah ya sa kwanakin mulkinka su ƙare, sun kuwa ƙare.
27 Ma'anar TEKEL ita ce an auna ka a ma'auni, aka tarar ka kāsa.
28 Ma'anar PERES ita ce an raba mulkinka, an ba mutanen Mediya da na Farisa.”
29 Sai Belshazzar ya ba da umarni, aka sa wa Daniyel rigar shunayya, aka sa sarƙar zinariya a wuyansa, aka kuma yi shela, cewa yanzu shi ne na uku cikin masu mulkin ƙasar.
30 A wannan dare kuwa aka kashe Belshazzar Sarkin Kaldiyawa.
31 Dariyus kuwa Bamediye ya karɓi mulkin, yana da shekara sittin da biyu.