1 Dariyus ya ga ya yi kyau ya naɗa muƙaddas guda ɗari da ashirin a dukan mulkinsa.
2 Sai ya naɗa Daniyel da waɗansu mutum biyu su zama shugabannin muƙaddasan nan. Su muƙaddasan kuwa za su riƙa ba shugabannin labarin aikinsu, don kada sarki ya yi hasarar kome.
3 Sai Daniyel ya shahara fiye da sauran shugabannin, da su muƙaddasan, domin yana da nagarin ruhu a cikinsa. Sarki kuwa ya shirya ya gabatar da shi kan dukan mulkin.
4 Sai shugabannin, da su muƙaddasan suka nemi Daniyel da laifi game da ayyukan mulki, amma ba su sami laifin da za su tuhume shi da shi ba, domin shi amintacce ne, ba shi da kuskure ko ha'inci.
5 Sai mutanen nan suka ce, “Ba za mu sami Daniyel da laifin da za mu kama shi da shi ba, sai dai ko mu neme shi da laifi wajen dokokin Allahnsa.”