13 “A cikin wahayi na dare, na ga wani kamar Ɗan Mutum.Yana zuwa cikin gizagizai,Ya zo wurin wanda yake Tun Fil Azal,Aka kai shi gabansa.
14 Aka kuwa danƙa masa mulki, da ɗaukaka, da sarauta,Domin dukan jama'a, da al'ummai, da harsuna su bauta masa.Mulkinsa, madawwamin mulki ne,Wanda ba zai ƙare ba.Sarautarsa ba ta tuɓuwa.”
15 “Amma ni Daniyel raina ya damu, wahayin da na gani ya tsorata ni.
16 Sai na matsa kusa da ɗaya daga cikin waɗanda suke tsaye a wurin, na tambaye shi ma'anar waɗannan abubuwa duka. Sai ya bayyana mini, ya kuma ganar da ni ma'anar waɗannan abubuwa.
17 Waɗannan manyan dabbobi guda huɗu, sarakuna ne huɗu waɗanda za su taso a duniya.
18 Amma tsarkaka na Maɗaukaki za su karɓi mulki, su kuwa riƙe mulkin har abada abadin.
19 “Sai na nemi in san ainihin ma'anar dabba ta huɗu, wadda ta bambanta da sauran. Tana da bantsoro ƙwarai, tana kuma da haƙoran baƙin ƙarfe da faratan tagulla. Ta cinye, ta ragargaje, sa'an nan ta tattake sauran da ƙafafunta.