9 Sarauniya Bashti kuma ta yi wa mata babban biki a fādar sarki Ahasurus.
10 A rana ta bakwai sa'ad da zuciyar sarki take murna saboda ruwan inabi, sai ya umarta bābāninsa guda bakwai, waɗanda suke yi masa hidima, wato Mehuman, da Bizta, da Harbona, da Bigta, da Abagta, da Zetar, da Karkas,
11 su kirawo sarauniya Bashti ta zo wurinsa da kambin sarauta, don ya nuna wa jama'a da shugabanni kyanta, gama ita kyakkyawa ce.
12 Amma sarauniya Bashti ta ƙi zuwa kamar yadda sarki ya umarci bābānin su faɗa mata. Wannan ya sa sarki ya husata ƙwarai.
13 Sarki kuwa ya nemi shawara ga masu hikima waɗanda suka ƙware zamani, gama sarki ya saba da yin haka ga waɗanda suka san doka da shari'a.
14 Su ne mutanen da suke kusa da shi, wato Karshena, da Shetar, da Admata, da Tarshish, da Meres, da Marsena, da Memukan. Su ne sarakuna bakwai na Farisa da Mediya, su ne masu zuwa wurin sarki, su ne kuma na fari a mulkin.
15 Sarki ya ce, “Bisa ga doka, me za a yi da sarauniya Bashti da yake ba ta yi biyayya da umarnin da na aika ta hannun babani ba?”