1 Bayan waɗannan abubuwa, sa'ad da sarki Ahasurus ya huce daga fushinsa, sai ya tuna da abin da Bashti ta yi, da dokar da aka yi a kanta.
2 Sa'an nan barorin sarki waɗanda suke yi masa hidima suka ce masa, “Bari a samo wa sarki 'yan mata, budurwai, kyawawa.
3 Bari kuma sarki ya sa shugabanni a cikin dukan lardunan mulkinsa su tara dukan kyawawan 'yan mata, budurwai, a gidan matan kulle a masarauta a Shushan, ƙarƙashin Hegai bābā na sarki, wanda yake lura da mata. A riƙa ba budurwan man shafawa.
4 Bari sarki ya zaɓi budurwar da ta gamshe shi, ta zama sarauniya maimakon Bashti.”Sarki fa ya ji daɗin wannan shawara, ya kuwa yi haka ɗin.