1 Bayan waɗannan abubuwa, sa'ad da sarki Ahasurus ya huce daga fushinsa, sai ya tuna da abin da Bashti ta yi, da dokar da aka yi a kanta.
2 Sa'an nan barorin sarki waɗanda suke yi masa hidima suka ce masa, “Bari a samo wa sarki 'yan mata, budurwai, kyawawa.
3 Bari kuma sarki ya sa shugabanni a cikin dukan lardunan mulkinsa su tara dukan kyawawan 'yan mata, budurwai, a gidan matan kulle a masarauta a Shushan, ƙarƙashin Hegai bābā na sarki, wanda yake lura da mata. A riƙa ba budurwan man shafawa.
4 Bari sarki ya zaɓi budurwar da ta gamshe shi, ta zama sarauniya maimakon Bashti.”Sarki fa ya ji daɗin wannan shawara, ya kuwa yi haka ɗin.
5 Akwai wani Bayahude a masarauta a Shushan, mai suna Mordekai ɗan Yayir, ɗan Shimai, ɗan Kish mutumin Biliyaminu.
6 An kamo shi a Urushalima tare 'yan zaman talala waɗanda aka kwashe tare da Yekoniya Sarkin Yahuza, wanda Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya kai su zaman talala.
7 Mordekai ne ya goyi Hadassa, wato Esta, 'yar kawunsa, gama ita marainiya ce. Ita kuwa kyakkyawa ce. Sa'ad da iyayenta suka rasu, sai Mordekai ya karɓe ta tankar 'yarsa.