20 Har yanzu dai Esta ba ta bayyana asalin danginta da mutanenta ba, kamar yadda Mordekai ya umarce ta, gama Esta tana yi wa Mordekai biyayya kamar ta yi tun lokacin da yake renonta.
21 A kwanakin nan sa'ad da Mordekai yake zaune a ƙofar sarki, sai babani biyu na sarki, wato Bigtana da Teresh waɗanda suke tsaron ƙofar, suka yi fushi, har suka nema su kashe sarki Ahasurus.
22 Wannan maƙarƙashiya ta sanu ga Mordekai, shi kuwa ya faɗa wa sarauniya Esta. Esta kuma ta faɗa wa sarki da sunan Mordekai.
23 Sa'ad da aka bincika al'amarin aka tarar haka yake. Sai aka rataye mutum biyu ɗin a kan gumagumai. Aka kuma rubuta labarin a littafin tarihi a gaban sarki.