1 Bayan waɗannan abubuwa, sai sarki Ahasurus ya gabatar da Haman ɗan Hammedata Ba'agage. Ya fīfita shi bisa dukan sarakunan da suke tare da shi.
2 Dukan barorin sarki waɗanda suke a bakin ƙofar sarki suka rusuna suka yi wa Haman mubaya'a, gama sarki ya umarta a yi masa haka. Amma Mordekai bai rusuna ya yi masa mubaya'a ba.
3 Sai barorin sarki waɗanda suke a bakin ƙofar sarki suka ce wa Mordekai, “Me ya sa ka karya dokar sarki?”
4 Sa'ad da suka yi ta yi masa magana kowace rana, shi kuwa bai kasa kunne gare su ba, sai suka faɗa wa Haman, don su gani ko maganar Mordekai za ta tabbata, gama ya faɗa musu shi Bayahude ne.
5 Sa'ad da Haman ya ga Mordekai bai rusuna ya yi masa mubaya'a ba, sai ya husata.
6 Har ma ya ga a kashe Mordekai kaɗai, wannan bai isa ba. Da yake an faɗa masa asalin Mordekai, sai ya nema ya hallaka dukan Yahudawa, wato kabilar Mordekai, waɗanda suke a dukan mulkin Ahasurus.
7 A watan fari, wato watan Nisan, a shekara ta goma sha biyu ta sarautar sarki Ahasurus, sai suka yi ta jefa Fur, wato kuri'a, a gaban Haman kowace rana da kowane wata har kuri'a ta faɗo a kan watan goma sha biyu, wato watan Adar.