1 A wannan dare kuwa sarki ya kasa yin barci, sai ya umarta a kawo littafin da aka rubuta al'amuran da suke faruwa don tunawa. Aka kuwa kawo, aka karanta wa sarki.
2 Sai aka tarar an rubuta yadda Mordekai ya gano maƙarƙashiyar Bigtana da Teresh, biyu daga cikin bābāni na sarki, masu tsaron ƙofa, waɗanda suka yi niyya su kashe sarki Ahasurus.
3 Sai sarki ya ce, “To, wace irin daraja ko girma aka ba Mordekai saboda wannan?”Barorin sarki waɗanda suke yi masa hidima suka ce, “Ba a yi masa kome ba.”
4 Sarki kuwa ya ce, “Wane ne yake a shirayi?”Daidai lokacin ne kuwa Haman ya shigo shirayi na fari na fādar sarki, don ya yi magana da sarki a kan a rataye Mordekai a gungumen itace da ya shirya.
5 Barorin sarki suka ce, “Ai, Haman ne yake tsaye a shirayi.”Sai sarki ya ce ya shigo.
6 Da shigowar Haman, sai sarki ya ce masa, “Me za a yi wa mutumin da sarki yake so ya ɗaukaka?”Haman ya yi tunani ya ce a ransa, “Wane ne sarki yake so ya ɗaukaka, in banda ni?”
7 Sai Haman ya ce wa sarki, “Abin da za a yi wa wanda sarki yake so ya ɗaukaka ke nan.