1 A wannan rana sai sarki Ahasurus ya ba Esta gidan Haman, maƙiyin Yahudawa, da duk dukiyar Haman. Mordekai kuwa ya zo gaban sarki, gama Esta ta bayyana yadda yake a gare ta.
2 Sa'an nan sarki ya ɗauki zobensa na hatimi, wanda ya karɓe a wurin Haman, ya ba Mordekai. Esta kuma ta ba Mordekai gidan Haman.
3 Sa'an nan kuma Esta ta faɗi a wajen ƙafafun sarki, ta roƙe shi da hawaye ya kawar da mugun shirin da Haman Ba'agage ya shirya wa Yahudawa.
4 Sai sarki ya miƙo wa Esta sandan sarauta na zinariya.
5 Esta kuwa ta miƙe tsaye a gaban sarki, ta ce, “Idan sarki ya yarda, idan kuma na sami tagomashi a wurinka, idan ya yi wa sarki kyau, idan kuma sarki yana jin daɗina, bari a yi rubutu a soke wasiƙun da Haman Ba'agage ɗan Hammedata ya rubuta don a hallaka Yahudawan da suke cikin dukan lardunan sarki.
6 Gama ƙaƙa zan iya daurewa da ganin masifa da hallaka na mutanena da dangina?”