11 To, sai suka ce mana, ‘Mu bayin Allah ne wanda yake da sama da ƙasa, muna sāke gina Haikalin da wani babban sarki na Isra'ila ya gina tun shekaru da yawa da suka wuce.
12 Amma saboda kakanninmu suka tsokani Allah na Sama, sai ya bashe su a hannun Nebukadnezzar, Sarkin Babila, mutumin Kaldiya. Shi ne ya lalatar da Haikalin nan, ya kuma kwashe jama'a zuwa Babila.
13 Amma a shekara ta fari ta sarautar Sairus, Sarkin Babila, sai ya ba da izini a sāke gina wannan Haikali na Allah.
14 Kwanonin zinariya da na azurfa na Haikalin Allah, waɗanda Nebukadnezzar ya kwashe daga cikin Haikalin da yake Urushalima, zuwa haikalin gumaka na Babila, sarki Sairus ya ɗauke su daga haikalin Babila ya ba wani mai suna Sheshbazzar wanda ya naɗa shi mai mulki.
15 Ya ce masa, ya ɗauki waɗannan kwanoni, ya tafi, ya sa su cikin Haikalin da yake a Urushalima, a sāke gina Haikalin Allah a wurin da yake a dā.’
16 Sheshbazzar kuwa ya zo ya aza harsashin ginin Haikalin Allah wanda yake a Urushalima. Tun daga wannan lokaci, har yanzu ana ta gininsa, har yanzu kuma ba a gama ba.
17 Domin haka in ya gamshi sarki, sai a bincike ɗakin littattafan da yake Babila don a gani ko sarki Sairus ya ba da izini a sāke gina wannan Haikalin Allah a Urushalima. Bari sarki ya aiko mana da abin da ya gani a kan wannan al'amari.”