4 da Zarahiya, da Uzzi, da Bukki,
5 da Abishuwa da Finehas, da Ele'azara, da Haruna babban firist.
6 Ezra ɗin ya taho daga Babila. Shi malami ne, masanin shari'ar Musa, wadda Ubangiji Allah na Isra'ila ya bayar. Sarki kuwa ya ba shi dukan abin da ya roƙa, gama Ubangiji Allahnsa yana tare da shi.
7 A shekara ta bakwai kuma ta sarautar sarki Artashate, waɗansu mutanen Isra'ila, da waɗansu firistoci, da Lawiyawa,da mawaƙa, da matsaran ƙofa, da ma'aikatan Haikali, suka taho Urushalima.
8 Ezra kuma tare da su, suka iso Urushalima a watan biyar na shekara ta bakwai ta sarautar sarkin.
9 Suka taso daga Babila a rana ta fari ga watan fari, suka iso Urushalima a rana ta fari ga watan biyar, Allah kuwa yana tare da su.
10 Gama Ezra ya ba da kansa ga yin nazarin dokokin Allah, ya kiyaye su, ya kuma koyar wa Isra'ilawa dokoki da farillan Allah.