1 A sa'ad da Allah ya fara halittar Sama da duniya,
2 duniya ba ta da siffa, sarari ce kawai, duhu kuwa yana lulluɓe da fuskar zurfin teku, Ruhun Allah kuma yana shawagi bisa ruwayen.
3 Allah ya ce, “Bari haske ya kasance,” sai kuwa ya kasance.
4 Allah ya ga hasken yana da kyau. Allah ya raba tsakanin hasken da duhu,
5 ya ce da hasken, “Yini,” duhu kuwa, “Dare.” Ga maraice, ga safiya, kwana ɗaya ke nan.
6 Allah ya ce, “Bari sarari ya kasance tsakanin ruwaye, don ya raba tsakaninsu.”
7 Allah kuwa ya yi sarari, ya kuma raba tsakanin ruwayen da suke ƙarƙashin sararin da ruwayen da suke birbishin sararin. Haka nan kuwa ya kasance.