Far 38 HAU

Yahuza da Tamar

1 Ya zama fa a wannan lokaci, Yahuza ya bar 'yan'uwansa ya gangara, ya zauna wurin wani Ba'adullame mai suna Hira.

2 A can, sai Yahuza ya ga 'yar wani Bakan'ane mai suna Shuwa. Ya aure ta, ya shiga wurinta,

3 ta yi ciki, ta haifi ɗa namiji, ya kuwa raɗa masa suna Er.

4 Sai ta sāke yin ciki, ta kuma haifi ɗa, ta raɗa masa suna Onan.

5 Har yanzu kuma ta sāke haihuwar ɗa, ta raɗa masa suna Shela. A Kezib ta haifi Shela.

6 Yahuza kuwa ya auro wa ɗan farinsa, Er, mata, sunanta Tamar.

7 Amma Er, ɗan farin Yahuza mugu ne a gaban Ubangiji. Sai Ubangiji ya kashe shi.

8 Sa'an nan Yahuza ya ce wa, Onan, “Shiga wurin matar ɗan'uwanka, ka yi mata wajibin ɗan'uwan miji, ka samar wa ɗan'uwanka zuriya.”

9 Amma Onan ya sani zuriyar ba za ta zama tasa ba, saboda haka duk lokacin da ya shiga wurin matar ɗan'uwansa, sai ya zubar da maniyyi a ƙasa don kada ya ba ɗan'uwansa zuriya.

10 Amma abin nan da ya yi, mugun abu ne a gaban Ubangiji, shi ma Ubangiji ya kashe shi.

11 Yahuza kuwa ya ce wa Tamar surukarsa, “Yi zaman gwauranci a gidan mahaifinki, har ɗana Shela ya yi girma,” gama yana jin tsoro kada shi kuma ya mutu kamar 'yan'uwansa. Saboda haka Tamar ta tafi ta zauna a gidan mahaifinta.

12 A kwana a tashi, ga matar Yahuza, 'yar Shuwa ta rasu. Da Yahuza ya gama karɓar ta'aziyya, sai ya haura Timna wurin masu sausayar tumakinsa, da shi da abokinsa Hira Ba'adullame.

13 Sa'ad da aka faɗa wa Tamar, aka ce, “Surukinki zai haura zuwa Timna ya yi wa tumakinsa sausaya,”

14 sai ta tuɓe tufafinta na takaba, ta yi lulluɓi ta lulluɓe kanta, ta zauna a ƙofar Enayim a hanyar Timna, gama ta ga Shela ya yi girma, amma ba a ba da ita gare shi ba.

15 Da Yahuza ya gan ta, ya yi tsammani wata karuwa ce, gama ta rufe fuskarta.

16 Sai ya je wurinta a gefen hanyar, ya ce, “Zo, mu kwana mana,” gama bai san ita surukarsa ba ce.Sai ta ce, “Me za ka ba ni, da za ka kwana da ni?”

17 Ya amsa, ya ce, “Zan aiko miki da ɗan akuya daga cikin garken.”Ta ce, “Ko ka ba ni jingina, kafin ka aiko?”

18 Ya ce, “Wane alkawari zan yi miki?”Ta amsa, ta ce, “Ba ni hatiminka da ɗamararka da sandan da yake a hannunka.” Ya kuwa ba ta su, ya kwana da ita. Sai ta yi ciki.

19 Ta tashi ta yi tafiyarta. Da ta cire lulluɓinta ta sa tufafinta na takaba.

20 Sa'ad da Yahuza ya aika da ɗan akuya ta hannun abokinsa Ba'adullame don ya karɓi jinginar daga hannun matar, bai same ta ba.

21 Ya tambayi mutanen wurin, ya ce, “Ina karuwan nan wadda take zaune a Enayim a bakin hanya?”Sai suka ce, “Ba wata karuwar da ta taɓa zama nan.”

22 Ya koma wurin Yahuza ya ce, “Ban same ta ba, mutanen wurin kuma suka ce, ‘Ba wata karuwa da ta zo nan.’ ”

23 Yahuza ya amsa, ya ce, “Bari ta riƙe abubuwan su zama nata, don kada a yi mana dariya, gama ga shi, na aike da ɗan akuya, amma ba ka same ta ba.”

24 Bayan misalin wata uku, aka faɗa wa Yahuza, “Tamar surukarka ta yi lalata, har ma tana da ciki.”Sai Yahuza ya ce, “A fito da ita, a ƙone ta.”

25 Za a fito da ita ke nan sai ta aika wa surukinta, ta ce, “Wanda yake da waɗannan kaya shi ya yi mini ciki.” Ta kuma ce, “Ka shaida, ina roƙonka, ko na wane ne wannan hatimi, da abin ɗamarar, da sanda.”

26 Sai Yahuza ya shaida su, ya ce, “Ta fi ni gaskiya, tun da yake ban ba da ita ga ɗana Shela ba.” Daga nan bai ƙara kwana da ita ba.

27 Sa'ad da lokaci ya yi da za ta haihu, ashe, cikin tagwaye ne.

28 Da tana cikin naƙuda, sai hannun wani ya fara fitowa, ungozoma kuwa ta ɗauki jan zare ta ɗaura a hannun, tana cewa, “Wannan shi ya fara fitowa.”

29 Amma da ya janye hannunsa, ga ɗan'uwansa ya fito, sai ta ce, “A'a, ta haka za ka keta ka fito!” Saboda haka aka raɗa masa suna Feresa.

30 Daga baya ɗan'uwansa ya fito da jan zare a hannunsa, aka kuwa sa masa suna Zera.