14 Allah kuwa ya ce, “Bari haskoki su kasance a cikin sararin, su raba tsakanin yini da dare, su kuma zama alamu, da yanayi na shekara, da wokatai.
15 Bari kuma su zama haskoki a cikin sarari su haskaka duniya.” Haka nan kuwa ya kasance.
16 Allah kuwa ya yi manyan haskokin nan biyu, haske mafi girma ya mallaki yini, ƙaramin kuwa ya mallaki dare, ya kuma yi taurarin.
17 Allah ya sa su a cikin sarari su haskaka duniya,
18 su yi mulkin yini da kuma dare, su raba tsakanin haske da duhu. Allah kuwa ya ga yana da kyau.
19 Ga maraice, ga safiya, kwana na huɗu ke nan.
20 Allah kuwa ya ce, “Bari ruwaye su fid da ɗumbun masu rai, bari tsuntsaye kuma su riƙa tashi bisa duniya ƙarƙashin sarari.”