12 da Resen wadda take tsakanin Nineba da Kala, wato babban birni.
13 Mizrayim shi ne mahaifin Ludawa, da Anamawa, da Lehabawa, da Neftuhawa,
14 da Fatrusawa, da Kasluhawa (inda Filistiyawa suka fito) da kuma Kaftorawa.
15 Kan'ana ya haifi Sidon ɗan farinsa, da Het,
16 shi ne kuma mahaifin Yebusiyawa, da Amoriyawa, da Girgashiyawa,
17 da Hiwiyawa, da Arkiyawa, da Siniyawa,
18 da Arwadiyawa, da Zemarawa da Hamatiyawa. Bayan haka sai kabilan Kan'aniyawa suka yaɗu.