13 Arfakshad kuwa ya yi shekara arbaminya da uku bayan haihuwar Shela, ya kuma haifi 'ya'ya mata da maza.
14 Sa'ad da Shela yake da shekara talatin, ya haifi Eber,
15 Shela kuwa ya yi shekara arbaminya da uku bayan haihuwar Eber, ya kuma haifi 'ya'ya mata da maza.
16 Sa'ad da Eber ya yi shekara talatin da huɗu ya haifi Feleg,
17 Eber kuwa ya yi shekara arbaminya da talatin, bayan haihuwar Feleg, ya kuma haifi 'ya'ya mata da maza.
18 Sa'ad da Feleg ya yi shekara talatin ya haifi Reyu.
19 Feleg ya yi shekara metan da tara bayan haihuwar Reyu, ya kuma haifi 'ya'ya mata da maza.