23 Serug kuwa ya yi shekara metan bayan haihuwar Nahor, ya kuma haifi 'ya'ya mata da maza.
24 Sa'ad da Nahor ya yi shekara ashirin da tara, ya haifi Tera,
25 Nahor kuwa ya yi shekara ɗari da goma sha tara bayan haihuwar Tera, ya kuma haifi 'ya'ya mata da maza.
26 Sa'ad da Tera ya yi shekara saba'in, ya haifi Abram, da Nahor, da Haran.
27 Yanzu dai waɗannan su ne zuriyar Tera, Tera ya haifi Abram, da Nahor, da Haran, Haran kuwa shi ne ya haifi Lutu.
28 Haran kuwa ya rasu a idon mahaifinsa Tera a ƙasar haihuwarsa, a Ur ta Kaldiyawa.
29 Da Abram da Nahor suka yi aure, sunan matar Abram Saraya, sunan matar Nahor kuwa Milka, ita 'yar Haran ce, mahaifin Milka da Iskaya.