1 Domin haka Abram ya bar Masar zuwa Negeb, shi da matarsa, da abin da yake da shi duka tare da Lutu.
2 Yanzu Abram ya arzuta da dabbobi, da azurfa, da zinariya.
3 Ya yi ta tafiya daga Negeb har zuwa Betel, har wurin da ya kafa alfarwarsa da fari, tsakanin Betel da Ai,
4 a inda dā ya gina bagade. A can Abram ya kira bisa sunan Ubangiji.
5 Lutu wanda ya tafi tare da Abram, shi kuma yana da garkunan tumaki, da na shanu, da alfarwai,
6 domin haka ƙasar ba ta isa dukansu biyu su zauna tare ba, saboda mallakarsu ta cika yawa, har da ba za su iya zama tare ba.