2 Sai Saraya ta ce wa Abram, “To, ga shi, Ubangiji ya hana mini haihuwar 'ya'ya. Shiga wurin baranyata, mai yiwuwa ne in sami 'ya'ya daga gare ta.” Abram kuwa ya saurari murya matarsa Saraya.
3 A lokacin nan kuwa Abram yana da shekara goma da zama a ƙasar Kan'ana sa'ad da Saraya matar Abram ta ɗauki Hajaratu Bamasariya, baranyarta, ta bai wa Abram mijinta ta zama matarsa.
4 Abram kuwa ya shiga wurin Hajaratu, ta kuwa yi ciki. Da ta ga ta sami ciki sai ta dubi uwargijiyarta a raine.
5 Sai Saraya ta ce wa Abram, “Bari cutar da aka cuce ni da ita ta koma kanka! Na ba da baranyata a ƙirjinka, amma da ta ga ta sami ciki, sai tana dubana a raine. Ubangiji ya shara'anta tsakanina da kai.”
6 Amma Abram ya ce wa Saraya, “Ga shi, baranyarki tana cikin ikonki, yi yadda kika ga dama da ita.” Saraya ta ƙanƙanta ta, sai Hajaratu ta gudu daga gare ta.
7 Mala'ikan Ubangiji kuwa ya sami Hajaratu a gefen wata maɓuɓɓugar ruwa a jeji, wato maɓuɓɓugar da take kan hanyar Shur.
8 Sai ya ce, “Ke Hajaratu, baranyar Saraya, ina kika fito, ina kuma za ki?”Ta ce, “Gudu nake yi daga uwargijiyata Saraya.”