4 Abram kuwa ya shiga wurin Hajaratu, ta kuwa yi ciki. Da ta ga ta sami ciki sai ta dubi uwargijiyarta a raine.
5 Sai Saraya ta ce wa Abram, “Bari cutar da aka cuce ni da ita ta koma kanka! Na ba da baranyata a ƙirjinka, amma da ta ga ta sami ciki, sai tana dubana a raine. Ubangiji ya shara'anta tsakanina da kai.”
6 Amma Abram ya ce wa Saraya, “Ga shi, baranyarki tana cikin ikonki, yi yadda kika ga dama da ita.” Saraya ta ƙanƙanta ta, sai Hajaratu ta gudu daga gare ta.
7 Mala'ikan Ubangiji kuwa ya sami Hajaratu a gefen wata maɓuɓɓugar ruwa a jeji, wato maɓuɓɓugar da take kan hanyar Shur.
8 Sai ya ce, “Ke Hajaratu, baranyar Saraya, ina kika fito, ina kuma za ki?”Ta ce, “Gudu nake yi daga uwargijiyata Saraya.”
9 Mala'ikan Ubangiji ya ce mata, “Koma wurin uwargijiyarki, ki yi mata ladabi.”
10 Mala'ikan Ubangiji kuma ya ce mata, “Zan riɓaɓɓanya zuriyarki ainun har da ba za a iya lasafta su ba saboda yawansu.”