23 Ibrahim kuwa ya ɗauki Isma'ilu ɗansa, da dukan bayi, haifaffun gidansa, da waɗanda aka sayo su da kuɗinsa, ya kuwa yi wa kowane namiji na jama'ar gidansa kaciyar loɓarsa a wannan rana bisa ga faɗar Allah.
24 Ibrahim na da shekara tasa'in da tara sa'ad da aka yi masa kaciyar loɓarsa.
25 Isma'ilu ɗansa yana ɗan shekara goma sha uku sa'ad da aka yi masa kaciya.
26 A wannan rana, Ibrahim da ɗansa Isma'ilu aka yi musu kaciya,
27 da mazajen gidansa duka, da waɗanda suke haifaffun gidan da waɗanda aka sayo da kuɗi daga baƙi, aka yi musu kaciya tare da shi.