12 Sai Saratu ta yi dariya a ranta, tana cewa, “Bayan na tsufa mai gidana kuma ya tsufa sa'an nan zan sami wannan gatanci?”
13 Ubangiji ya ce wa Ibrahim, “Me ya ba Saratu dariya, har da ta ce, ‘Ashe zan haifi ɗa, a yanzu da na riga na tsufa?’
14 Akwai abin da zai fi ƙarfin Ubangiji? A ajiyayyen lokaci zan komo wurinka, cikin wata tara, Saratu kuwa za ta haifi ɗa.”
15 Amma Saratu ta yi mūsu, tana cewa, “Ai, ban yi dariya ba,” Gama tana jin tsoro.Ya ce, “A'a, hakika kin yi dariya.”
16 Sai mutanen suka tashi daga wurin, suka fuskanci Saduma, Ibrahim kuwa ya yi musu rakiya ya sallame su.
17 Ubangiji ya ce, “Zan ɓoye wa Ibrahim abin da nake shirin aikatawa?
18 Ga shi kuwa, Ibrahim zai ƙasaita ya zama al'umma mai iko, sauran al'umman duniya duka za su sami albarka ta dalilinsa.