20 Sai kuma Ubangiji ya ce, “Tun da yake kuka a kan Saduma da Gwamrata ya yi yawa, zunubinsu kuma ya yi muni ƙwarai,
21 zan sauka in gani ko sun aikata kamar yadda kukan ya zo gare ni, zan bincike.”
22 Sa'an nan mutanen suka juya daga nan, suka nufi Saduma, amma Ibrahim ya tsaya a gaban Ubangiji.
23 Sai Ibrahim ya matso kusa, ya ce, “Ashe, za ka hallaka adali tare da mugun?
24 Da a ce, akwai masu adalci hamsin cikin birnin, za ka hallaka wurin, ba za ka yafe su saboda masu adalcin nan hamsin waɗanda suke cikinsa ba?
25 Wannan ya yi nesa da kai, da ka aikata irin haka, wato da za ka aza mai adalci daidai yake da mugu! Wannan ya yi nesa da kai! Mahukuncin dukan duniya ba zai yi adalci ba?”
26 Sai Ubangiji ya ce, “In na sami adalai hamsin a cikin birnin Saduma, zan yafe wa dukan wurin sabili da su.”