23 Da hantsi Lutu ya isa Zowar.
24 Sai Ubangiji ya yi ta zuba wa Saduma da Gwamrata wutar kibritu daga sama,
25 ya hallakar da waɗannan birane, da dukan kwarin, da dukan mazaunan biranen, da tsire-tsire.
26 Amma matar Lutu da take bin bayansa ta waiwaya, sai ta zama surin gishiri.
27 Da sassafe kuwa sai Ibrahim ya tafi wurin da dā ya tsaya a gaban Ubangiji,
28 ya duba wajen Saduma da Gwamrata, da wajen dukan ƙasar kwari, sai ya hangi, hayaƙi yana tashi kamar hayaƙin da yake fitowa daga matoya a bisa ƙasar.
29 Amma sa'ad da Allah ya hallaka biranen kwarin, ya tuna da Ibrahim, ya fid da Lutu daga halakar.