35 Saboda haka suka sa shi ya bugu da ruwan inabi a wannan dare kuma, ƙaramar ta shiga ta kwana da shi. Shi kuwa bai san da kwanciyarta ba balle fa tashinta.
36 Haka nan kuwa, 'ya'yan Lutu biyu ɗin nan suka sami ciki daga mahaifinsu.
37 Ta farin, ta haifi ɗa namiji, ta sa masa suna Mowab. Shi ne asalin Mowabawa har yau.
38 Ƙaramar kuma ta haifi ɗa namiji, ta sa masa suna Benammi, shi ne asalin Ammonawa har yau.