10 Abimelek kuma ya ce wa Ibrahim, “Me ya sa ka yi wannan abu?”
11 Ibrahim ya ce, “Na yi haka, domin ina zaton babu tsoron Allah ko kaɗan a wannan wuri, shi ya sa na zaci, kashe ni za a yi saboda matata.
12 Banda haka nan ma, hakika ita 'yar'uwata ce, 'yar mahaifina amma ba ta mahaifiyata ba ce. Na kuwa aure ta.
13 A lokacin da Allah ya raba ni da gidan mahaifina, ya sa ni yawace yawace, na ce mata, ‘Wannan shi ne alherin da za ki yi mini a duk inda muka je, ki ce da ni ɗan'uwanki ne.’ ”
14 Abimelek ya ɗauki tumaki da takarkarai, da bayi mata da maza, ya ba Ibrahim, ya kuma mayar masa da matarsa Saratu.
15 Abimelek kuwa ya ce, “Ga shi, ƙasata tana gabanka, ka zauna a duk inda ya yi maka daɗi.”
16 Ga Saratu kuwa ya ce, “Ga shi, na ba ɗan'uwanki azurfa guda dubu, shaida ce ta tabbatarwa a idanun dukan waɗanda suke tare da ke, da kuma a gaban kowa, cewa ba ki da laifi.”