13 A lokacin da Allah ya raba ni da gidan mahaifina, ya sa ni yawace yawace, na ce mata, ‘Wannan shi ne alherin da za ki yi mini a duk inda muka je, ki ce da ni ɗan'uwanki ne.’ ”
14 Abimelek ya ɗauki tumaki da takarkarai, da bayi mata da maza, ya ba Ibrahim, ya kuma mayar masa da matarsa Saratu.
15 Abimelek kuwa ya ce, “Ga shi, ƙasata tana gabanka, ka zauna a duk inda ya yi maka daɗi.”
16 Ga Saratu kuwa ya ce, “Ga shi, na ba ɗan'uwanki azurfa guda dubu, shaida ce ta tabbatarwa a idanun dukan waɗanda suke tare da ke, da kuma a gaban kowa, cewa ba ki da laifi.”
17 Ibrahim ya yi addu'a ga Allah, Allah kuwa ya warkar da Abimelek, da matarsa, da bayinsa mata, har kuma suka sami haihuwa.
18 Gama dā Allah ya kulle mahaifar dukan gidan Abimelek saboda Saratu matar Ibrahim.