10 Sai ta ce wa Ibrahim, “Ka kori wannan baiwa da ɗanta, gama ɗan baiwan nan ba zai zama magaji tare da ɗana Ishaku ba.”
11 Abin ya ɓata wa Ibrahim zuciya ƙwarai sabili da ɗansa.
12 Amma Allah ya ce wa Ibrahim, “Kada zuciyarka ta ɓaci saboda yaron da kuma baiwarka. Kome Saratu ta faɗa maka, ka yi yadda ta ce, gama ta wurin Ishaku za a riƙa kiran zuriyarka.
13 Zan kuma yi al'umma daga ɗan baiwar, domin shi ma zuriyarka ne.”
14 Ibrahim ya tashi da sassafe, ya kuma ɗauki gurasa da salkar ruwa, ya bai wa Hajaratu, ya ɗora kafaɗarta. Sai ya ba ta ɗanta, ya sallame ta. Ta tafi ta yi ta yawo cikin jejin Biyer-sheba.
15 Sa'ad da ruwan salkar ya ƙare, sai ta yar da yaron a ƙarƙashin wani ƙaramin itace.
16 Sai ta tafi, ta zauna ɗaura da shi da 'yar rata, misalin nisan harbin baka, gama ta ce, “Don kada in ga mutuwar yaron.” Da ta zauna can daura da shi, sai yaron ya ta da muryarsa ya yi ta kuka.