20 Allah kuwa yana tare da yaron, ya kuwa yi girma, ya zauna a jeji, ya zama riƙaƙƙen maharbi.
21 Ya zauna a jejin Faran. Sai mahaifiyarsa ta auro masa mata daga ƙasar Masar.
22 A lokacin nan fa, ya zamana Abimelek, da Fikol shugaban sojojinsa ya zo ya ce wa Ibrahim, “Allah yana tare da kai cikin sha'aninka duka,
23 don haka, yanzu sai ka rantse mini da Allah, cewa ba za ka ci amanata, ko ta 'ya'yana, ko ta zuriyata ba, amma kamar yadda na riƙe ka cikin mutunci, haka za ka yi da ni da ƙasar da ka yi baƙunta a ciki.”
24 Sai Ibrahim ya amsa, “I, zan rantse.”
25 Sa'ad da Ibrahim ya kawo kuka ga Abimelek a kan rijiyar ruwa wadda barorin Abimelek suka ƙwace,
26 Abimelek ya ce, “Ban san wanda ya yi wannan abu ba, ba ka faɗa mini ba, ban kuwa taɓa ji ba sai yau.”