25 Sa'ad da Ibrahim ya kawo kuka ga Abimelek a kan rijiyar ruwa wadda barorin Abimelek suka ƙwace,
26 Abimelek ya ce, “Ban san wanda ya yi wannan abu ba, ba ka faɗa mini ba, ban kuwa taɓa ji ba sai yau.”
27 Ibrahim ya ɗibi tumaki da takarkarai ya bai wa Abimelek, su biyu ɗin kuwa suka yi alkawari.
28 Ibrahim ya ware 'yan raguna bakwai daga cikin garke.
29 Abimelek ya ce wa Ibrahim, “Ina ma'anar waɗannan 'yan raguna bakwai da ka keɓe?”
30 Ya ce, “Waɗannan 'yan raguna bakwai za ka karɓe su daga hannuna domin su zama shaida a gare ni, cewa ni na haƙa rijiyan nan.”
31 Don haka aka kira wannan wuri Biyer-sheba, domin a can ne su duka suka yi rantsuwa.