1 Bayan waɗannan al'amura Allah ya jarraba Ibrahim ya ce masa, “Ibrahim!”Sai ya ce, “Ga ni.”
2 Ya ce, “Ɗauki ɗanka, tilon ɗanka Ishaku, wanda kake ƙauna, ka tafi ƙasar Moriya, a can za ka miƙa shi hadayar ƙonawa a bisa kan ɗayan duwatsun da zan faɗa maka.”
3 Sai Ibrahim ya tashi tun da sassafe, ya ɗaura wa jakinsa shimfiɗa ya kuwa ɗauki biyu daga cikin samarinsa tare da shi, da kuma ɗansa Ishaku, ya faskara itace na yin hadayar ƙonawa. Ya kuwa tashi ya tafi inda Allah ya faɗa masa.
4 A rana ta uku Ibrahim ya ta da idanunsa ya hangi wurin daga nesa.