20 Ana nan bayan waɗannan al'amura, aka faɗa wa Ibrahim, “Ga shi, Milka ta haifa wa ɗan'uwanka Nahor, 'ya'ya.
21 Uz ɗan fari, da Buz ɗan'uwansa, da Kemuwel mahaifin Aram,
22 da Kesed, da Hazo, da Fildash, da Yidlaf, da Betuwel.”
23 Betuwel kuwa ya haifi Rifkatu, su takwas ɗin nan Milka ta haifa wa Nahor, ɗan'uwan Ibrahim.
24 Banda haka, ƙwarƙwararsa, mai suna Reyuma, ta haifi Teba, da Gaham, da Tahash, da Ma'aka.