5 Ibrahim ya ce wa samarinsa, “Ku tsaya nan wurin jakin, ni da saurayin za mu yi gaba mu yi sujada, sa'an nan mu komo wurinku.”
6 Ibrahim ya ɗauki itacen hadayar ƙonawa, ya ɗora wa ɗansa Ishaku, shi kuma ya ɗauki wuta da wuƙa a hannunsa. Dukansu biyu kuwa suka tafi tare.
7 Ishaku ya ce wa mahaifinsa Ibrahim, “Baba!”Sai ya ce, “Ga ni, ɗana.”Ya ce, “Ga wuta, ga itace, amma ina ragon hadayar ƙonawa?”
8 Ibrahim ya ce, “Allah zai tanada wa kansa ragon hadayar ƙonawa, ya ɗana.” Sai su biyu suka tafi tare.
9 Sa'ad da suka zo wurin da Allah ya faɗa masa, sai Ibrahim ya gina bagade a can, ya jera itace a kai. Ya ɗaure Ishaku ɗansa, ya sa shi a bisa itacen bagaden.
10 Sai Ibrahim ya miƙa hannu ya ɗauki wuƙar don ya yanka ɗansa.
11 Amma mala'ikan Ubangiji ya yi kiransa daga sama, ya ce, “Ibrahim, Ibrahim!”Sai ya ce, “Ga ni.”