1 Yanzu Ibrahim ya tsufa, ya kuwa kwana biyu. Ubangiji kuma ya sa wa Ibrahim albarka a cikin abu duka.
2 Ibrahim ya ce wa baransa, daɗaɗɗen gidansa wanda yake hukunta dukan abin da yake da shi, “Sa hannunka a ƙarƙashin cinyata,
3 ka rantse da Ubangiji na sama da duniya, cewa ba za ka auro wa ɗana mata daga 'yan matan Kan'aniyawa waɗanda nake zaune a tsakaninsu ba.
4 Amma za ka tafi ƙasata, daga cikin dangina ka auro wa ɗana Ishaku mata.”
5 Sai baransa ya ce masa, “Watakila matar ba za ta yarda ta biyo ni zuwa wannan ƙasa ba, tilas ke nan, in koma da ɗanka ƙasar da ka fito?”
6 Ibrahim ya ce masa, “Ka kiyaye wannan fa, kada ka kuskura ka koma da ɗana can.
7 Ubangiji Allah na Sama wanda ya ɗauke ni daga gidan mahaifina daga ƙasar haihuwata, wanda ya yi magana da ni ya kuma rantse mini, ‘Ga zuriyarka zan ba da wannan ƙasa,’ shi zai aiki mala'ikansa a gabanka. Za ka kuwa auro wa ɗana mata daga can.