22 Sa'ad da raƙuman suka gama sha, mutumin ya ɗauki zoben zinariya mai nauyin rabin shekel, ya sa mata a hanci. Ya kuma ɗauki mundaye biyu na shekel goma na zinariya ya sa a hannuwanta,
23 ya ce, “Ki faɗa mini ke 'yar gidan wace ce? Akwai masauki a gidan mahaifinki inda za mu sauka?”
24 Sai ta ce masa, “Ni 'yar Betuwel ce ɗan Milka wanda ta haifa wa Nahor.”
25 Ta ƙara da cewa, “Muna da isasshen baro da harawa duka, da kuma masauki.”
26 Mutumin ya yi ruku'u ya yi wa Ubangiji sujada,
27 ya ce, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji na maigidana Ibrahim, wanda bai daina nuna madawwamiyar ƙaunarsa da amincinsa ga maigidana ba. Ubangiji ya bi da ni har zuwa gidan ɗan'uwan maigidana.”
28 Budurwar ta sheƙa a guje zuwa gida wurin mahaifiyarta ta faɗi waɗannan abubuwa.