1 Ibrahim ya auro wata mace kuma, sunanta Ketura.
2 Ta haifa masa Zimran, da Yokshan, da Medan, da Madayana, da Yisbak, da Shuwa.
3 Yokshan ya haifi Sheba da Dedan. 'Ya'yan Dedan su ne Asshurim, da Letushim, da Le'umomim.
4 'Ya'yan Madayana su ne Efa, da Efer, da Hanok, da Abida, da Eldaya. Waɗannan duka 'ya'yan Ketura ne.
5 Ibrahim ya ba Ishaku dukan abin da yake da shi.
6 Amma ga 'ya'yan ƙwaraƙwarai Ibrahim ya ba da kyautai, ya sallame su tun yana da rai, su tafi nesa da Ishaku zuwa can cikin ƙasar gabas.
7 Waɗannan su ne kwanakin shekarun Ibrahim a duniya, shekara ɗari da saba'in da biyar.