6 Amma ga 'ya'yan ƙwaraƙwarai Ibrahim ya ba da kyautai, ya sallame su tun yana da rai, su tafi nesa da Ishaku zuwa can cikin ƙasar gabas.
7 Waɗannan su ne kwanakin shekarun Ibrahim a duniya, shekara ɗari da saba'in da biyar.
8 Ibrahim ya ja numfashinsa na ƙarshe ya kuwa rasu cikin kyakkyawan tsufa, tsoho ne mai shekaru masu yawa, aka kai shi ga jama'arsa, waɗanda suka riga shi.
9 Ishaku da Isma'ilu 'ya'yansa suka binne shi a kogon Makfela a saurar Efron ɗan Zohar Bahitte, gabashin Mamre,
10 wato saurar da Ibrahim ya saya a wurin Hittiyawa. Can ne aka binne Ibrahim gab da Saratu matarsa.
11 Bayan rasuwa Ibrahim, Allah ya sa wa Ishaku ɗansa albarka. Ishaku kuwa ya zauna a Biyer-lahai-royi.
12 Waɗannan su ne zuriyar Isma'ilu ɗan Ibrahim, wanda Hajaratu Bamasariya, baranyar Saratu, ta haifa wa Ibrahim.