2 Ubangiji kuwa ya bayyana gare shi, ya ce, “Kada ka gangara zuwa Masar, ka zauna a ƙasar da zan faɗa maka.
3 Ka yi baƙunci cikin wannan ƙasa, ni kuwa zan kasance tare da kai, zan sa maka albarka, gama a gare ka da zuriyarka ne na ba da waɗannan ƙasashe, zan kuwa cika rantsuwar da na yi wa Ibrahim mahaifinka.
4 Zan riɓaɓɓanya zuriyarka kamar taurarin sararin sama, zan kuwa ba zuriyarka dukan waɗannan ƙasashe, ta wurin zuriyarka kuma al'umman duniya duka za su sami albarka,
5 saboda Ibrahim ya yi biyayya da muryata, ya kuma kiyaye umarnina, da dokokina, da ka'idodina, da shari'una.”
6 Ishaku ya yi zamansa a Gerar.
7 Sa'ad da mutanen wurin suka tambaye shi matarsa, ya ce, “Ita 'yar'uwata ce,” gama yana jin tsoro ya ce, “Ita matata ce,” don kada mutanen wurin su kashe shi saboda Rifkatu, da yake ita kyakkyawa ce.
8 Sa'ad da ya dakata 'yan kwanaki a can, sai Abimelek, Sarkin Filistiyawa ya duba ta taga, ya ga Ishaku ya rungumi Rifkatu.